Kafin cikar wa’adin da hukumar zaɓe ta kasa a Najeriya ta tsayar na miƙa sunayen ‘yan takara, a yanzu jam’iyyu 16 cikin 18 sun fitar da sunayen mutanen da za su musu takarar shugaban kasa.
Jam’iyyu biyu, wato African Democratic Party, ADP; da Action Peoples Party, APP, su suka saura su bayyana sunayen ‘yan takararsu.
Manyan Jam’iyyun da zuwa yanzu aka san ‘yan takararsu sun hada da jam’iyya mai mulki ta APC, da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sai kuma Labour Party, LP; da sabuwar jam’iyya New Nigerian Peoples Party, NNPP.
Ga jeren sunayen ‘yan takarar a jam’iyyu daban-daban
*Atiku Abubakar, Peoples Democratic Party, PDP
*Bola Ahmed Tinubu, All Progressives Congress, APC
*Peter Obi, Labour Party, LP
*Yusuf Mamman Dantalle Allied People’s Movement, APM
*Musa Kwankwaso, New Nigeria Peoples Party, NNPP
*Chekwas Okorie, All Progressives Grand Alliance, APGA
*Kola Abiola, Peoples Redemption Party, PRP
*Omoyele Sowore, African Action Congress, AAC
*Adewole Adebayo Social Democratic Party, SDP
*Dumebi Kachikwu, African Democratic Congress, ADC
*Okwudili Nwa-Anyajike, National Rescue Movement, NRM
*Dan Nwanyanwu, Zenith Labour Party, ZLP
*Christopher Imumolen, Accord
*Hamza Al-Mustapha, Action Alliance, AA
* Malik Ado-Ibrahim, Young Progressive Party, YPP
* Sunday Adenuga, Boot Party, BP. In ji BBC.