Jam’iyyar Republican na kan hanyar ƙwace iko da majalisar dattawan Amurka, kamar yadda abokiyar ƙawancen BBC, CBS ta yi hasashe.
Har yanzu ana fafatawa a sakamakon kujerun majalisar, to amma bisa ga dukkan alamu jam’iyyar Democrats ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar.
Bisa bayanana da ake da su, jam’iyyar ta kasa kayar da ɗan majalisar West Texas, wanda ke cikin wuraren da take fatan samun nasara