fidelitybank

Jam’iyyar mu za ta kwace dukannin sauran jihohin kasar nan – APC

Date:

Olatunbosun Oyintiloye, jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Osun, ya ce nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben gwamnan jihar Ondo alama ce ta cewa za ta kara kwace wasu jihohi.

Oyintiloye, mamba a kwamitin masu ruwa da tsaki na yakin neman zaben jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Osogbo yayin da yake mayar da martani kan nasarar da jam’iyyar ta samu.

Ya bayyana cewa tare da gagarumin goyon baya da kuri’un da ake baiwa jam’iyyar da dan takararta, Gwamna Lucky Ayedatiwa, ya kamata jihohin ‘yan adawa su yi shirin shan kaye a zabensu.

Oyintiloye ya jaddada cewa kuri’u 366,781 da APC ta samu, yayin da 117,845 dan takarar jam’iyyar PDP, Mista Agboola Ajayi ya yi, ya kasance mai kawo sauyi ga zabe mai zuwa a wasu jihohi.

A cewarsa, kamar yadda masu zabe suka kada kuri’a ga APC a Edo, da kuma Ondo, ya kamata jihohin adawa su shirya ba jam’iyyar ta hanyar kuri’un jama’a.

Oyintiloye ya bayyana cewa nasarar da jam’iyyar ta samu a jihohin biyu, ya kuma nuna cewa har yanzu masu zabe da talakawa sun yi amanna da ajandar sabunta fata na Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa ko shakka babu shugaban kasa yana aiki dare da rana domin farfado da tattalin arzikin kasa domin amfanin talakawa.

“Kamar yadda aka yi hasashe a baya, dimbin kuri’un da APC ta samu a lokacin zaben za su firgita jam’iyyun adawa, musamman PDP, kuma hakan ya cika,” inji shi.

“Wannan nasarar da aka samu ya nuna cewa har yanzu talakawa da masu zabe a jihar Ondo na da yakinin APC da gwamnatin shugaba Tinubu.

“Wannan wata alama ce mai karfi cewa sauran jihohin da jam’iyyun adawa ke mulki za a mika su ga APC ta masu zabe.”

“Daga Kogi zuwa Edo yanzu kuma a Ondo. Anambra na jira, Ekiti da Osun za su zo na karshe a babban zaben.”

“APC na kara karfi a karkashin Tinubu, kuma dimbin nasarorin da jam’iyyar ta samu alama ce da har yanzu mutane sun yi imani da jam’iyyar da shugabanninta,” inji shi.

 

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp