Kwamared Jonathan Asake da Bashir Idris Aliyu ne suka zama ƴan takarar gwamna kuma mataimakin jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Kaduna a zaben 2023 mai zuwa.
A zaben fidda gwani da aka yi a Kaduna ranar Talata, wani dan takarar gwamna, Shunom Adiga, ya sauka daga mukaminsa.
Wakilai daga kananan hukumomi 23 na jihar sun amince da nadin Asake baki daya.