fidelitybank

Jam’iyyar LP ta nada tsohuwar ministar kudi a matsayin shugaba

Date:

Jam’iyyar adawa ta LP ta naɗa tsohuwar ministar kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin sabuwar shugabar riƙon ƙwarya ta jam’iyyar.

Haka kuma jam’iyyar ta sanar da naɗin tsohon mataimakin shugaban marasa rinjayen na majalisar dattawa ƙasar, Sanata Darlington Nwokocha a matsayin sakataren riƙo na jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma ɗora wa – kwamitin riƙon ƙwaryar mai mambobi 29 – alhakin gudanar da zaɓukan shugabannin jam’iyyar a matakai daban-daban cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ne dai ciki har da jagoran jam’iyyar kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa Peter Obi da mataimakinsa suka gudanar da taron naɗa kwamitin riƙo na jam’iyyar a gidan gwamnatin jihar Abia, kamar yadda sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar.

To sai dai ɓangaren shugaban jam’iyyar, Julius Abure ya yi watsi da zaman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka jagoranta, tare da naɗin Sanata Nenadi Usman, suna masu bayyana shi da wanda ya saɓa wa ƙa’ida.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp