Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar Labour (LP) ya gabatar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi.
Manyan jami’an jam’iyyar, wakilan kungiyar kwadago ta ƙasa da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, masu ruwa da tsaki, da dai sauransu, ne suka halarci bikin, wanda aka gudanar a ranar Juma’a a sakatariyar LP ta kasa, Abuja.
Obi ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a babban taronta na kasa a garin Asaba na jihar Delta a ranar 30 ga watan Mayu bayan da wasu masu neman tsayawa takara suka yi masa takara.
Da yake jawabi bayan karbar takardar shaidar, tsohon gwamnan jihar Anambra ya jaddada kudirinsa na ceto ‘yan Najeriya daga kangin talauci, rashin shugabanci, rashin tsaro da sauran kalubalen da suka dabaibaye kasar.