fidelitybank

Jam’iyyar LP da ta ke mulki a jihar Abia ta sha ka yi a dukkannin zaɓen ƙananan hukumomi 17

Date:

Jam’iyyar Labour da ke mulkin jihar Abia ta kasa cin ko da ɗaya daga ƙananan hukumomin jihar 17 a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jiya Asabar.

A maimakon haka jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP), ce ta cinye yawancin ƙananan hukumomin inda ta samu 15 daga cikin 17.

Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ce ta ci ragowar ƙananan hukumomin biyu – ƙaramar hukumar Ugwunagbo da kuma Osisioma Ngwa.

Shugaban hukumar zaɓen jihar, (ABSIEC), George Chima, shi ne ya bayyana sakamakon a ofishin hukumar da ke babban birnin jihar, Umuahia, a jiya Asabar.

Mista Chima, ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaɓen da ya ce sama da jam’iyyu 12 suka shiga, ya gudana.

Sakamakon rigimar da ake yi ta shugabancin jam’iyyar Labour a tarayya, ‘yantakarar da ake gani suna da goyon bayan gwamnan jihar Alex Otti, sun tsaya takara ne a jam’iyyar Zenith Labour Party, wadda ta ci kujeru 15 ɗin.

Shugabancin jam’iyyar Labour na ƙasa na fama da rikici inda ake da ɓangare biyu, na tsohuwar ministar kuɗi Sanata Nenadi Usman, da Gwamna Otti ke bi, da kuma ɓangaren Julius Abure.

bbc naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp