Hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ta sanar da Alex Otti na Jam’iyyar Labour a matsayin zababben gwamnan jihar Abia.
Inec ta bayyana haka ne kwana hudu bayan zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Dama hukumar Inec ta dakatar da sanar da sakamakon zaben ƙaramar hukumar Obingwa saboda takaddamar da ta biyo baya da kuma matsalolin da aka fuskanta a karamar hukumar.
Da wannan sakamako, dan takarar Jam’iyyar Labour Alex Otti ya doke abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP Okey Ahiwe bayan da ya kasance wanda ya fi samun kuri’u masu yawa.
Otti ya samu kuri’u 175,467 yayin da Ahiwe ya samu kuri’u 88,529.