Jam’iyyar Labour ta kori sakataren yada labaranta na kasa, Abayomi Arabambi, tare da rusa shugabannin jam’iyyar reshen jihar Ogun bisa zargin cin mutuncin jam’iyyar.
Wannan dai na zuwa ne kusan watanni biyu gabanin babban zaben shekarar 2023.
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa ya dauki matakin ne, biyo bayan rawar da suka taka wajen korar Doyin Okupe, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Obi-Datti.
A yayin taron gaggawa na jam’iyyar NWC a Abuja, ranar Juma’a, Umar Farouk, sakataren jam’iyyar Kwadago ta kasa, ya sanar da rusa reshen jihar Ogun, da tsige kakakin jam’iyyar tare da dakatar da shugabanta da sauran shugabannin jam’iyyar.
An ce kwamitin ya zartas da kuri’ar amincewa da shugabancin shugaban kwamitin na kasa Julius Abure, inda ya ce ya yi nazari kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake zarginsa da aikatawa ba tare da wani laifi ba.
Shugabannin jam’iyyar LP reshen jihar Ogun sun tsige Okupe da wasu ‘yan jam’iyyar 10 bisa zargin “rashin zama ‘ya’yan jam’iyyar, da nuna wariyar launin fata da siyasa.