Jam’iyyar Labour ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga a ofisoshin hukumar zaɓe da ke faɗin ƙasar kan ƙin ba ta damar duba na’urorin BVAS da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da su ranar 25 ga watan Fabrairu.
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peter Obi ya nemi kotu da ta hana INEC sake saita na’ororin BVAS da aka yi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasar.
To amma kotun ta bai wa INEC damar saita na’urorin tare da bai wa Obi damar duba kayayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da su.
Karanta Wannan: A na yunkurin kashe ni a Legas – Dan takarar LP
To sai dai kwanaki bayan hukuncin kotun mai magana da yawun kwamityin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Dr Yunusa Tanko ya zargi hukumar zaɓen da ƙin bin umarnin kotu.
“Yayin da muke magana a yanzu INEC ta zaɓi bin umarnin da kotu ta ba ta na sake saita na’urorin BVAS, aikin da take cikin yi yanzu haka, sannan kuma ta ƙi bin umarnin damar da kotun ta ba mu na duba kayyakin da aka gudanar da aikin zaɓen,” kamar yadda ya bayyana a sanarwar da ya fitar.
“Dan haka za mu kira magoya bayanmu da su gudanar da zanga-zangar lumana wadda doka ta amince da ita, a ofisoshin hukumar zaɓe da ke faɗin ƙasar nan”.
Ya ƙara da cewa abin da ya sa ba za su gudanar da zanga-zangar a kan titunan ƙasar ba, shi ne ba sa so a ɗauki zanga-zangar tasu a matsayin tayar da hankali.