Kafofin yaɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa, manyan jagororin jam’iyar Democrat sun buƙaci Shugaba Biden ya janye daga takarar shugaban ƙasa a karo na biyu.
Suna fargaba cewa jam’iyarsu ka iya rasa rinjaye a dukkan majalisun ƙasar.
Tsohuwar kakakin majalisar, Nancy Pelosi, da shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Hakeem Jeffries, sun ce sun tattauana da shugaban ƙasar a cikin kwanakin nan.
Wakilin BBC ya ce rashin nuna karsashi da taɓuka abin kirki a muhawarar ƴantakara ya sanya ana shakku kan cancantar Biden ɗin.
Bugu da ƙari, yanzu haka dai Shugaba Biden ya kamu da cutar korona.