Hukumar zabe mai zaman kanta a ƙasa INEC, ta bayyana Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.
A daren da ya gabata ne hukumar INEC ta ce Mista Oyebanji ya samu kuri’u 178,057.
Hakan ya sanya jam’iyyar All Progressive Congress ta zamo wadda ta samu kuri’u mafi yawa a zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekara ta 2022.
Dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party, Olusegun Oni, shi ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kuri’u 82,211.