Shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ƴansiyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Najeriya, wanda a cewarsa hakan zai taimaka waje hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai tsohon shugaban majalisar wakilan ƙasar ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani.
“Muna maraba da samar da haɗakar. Ai ba wannan ba ne karo na farko da aka samu haɗakar ƴansiyasar a wannan ƙasar tamu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa “a dimokuraɗiyya ana buƙatar hamayya mai ƙarfi, domin idan babu hamayya mai ƙarfi, za mu iya faɗawa siyasar jam’iyyar ɗaya,” in ji shi.
A Najeriya dai fitatun ƴan jam’iyyun hamayya irin su Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu ne suka haɗu a jam’iyyar ADC domin fuskantar zaɓen 2027, inda suke fata za su kayar da Bola Tinubu.