Tsohon gwamnan jihar Aambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya bayyana cewa, sabuwar jam’iyyarsa ta siyasa za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023 ta hanyar hada ma’aikata da dalibai domin kada kuri’a.
Obi ya zanta da manema labarai a Abeokuta, jihar Ogun ta bakin babban daraktan yakin neman zabensa, Dr. Doyin Okupe a wajen wani taro da shugabannin LP.
Ya kara da cewa jam’iyyar PDP da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sun kare kuma sun rasa nasaba da siyasa a kasar nan kuma za a iya kayar da su cikin sauki a zaben 2023.
Ya kara da cewa jiga-jigan jam’iyyar PDP sun ɗimauce, sakamakon kin amincewa da tsayar da tikitin takarar shugaban kasa a 2023 zuwa Kudancin kasar nan.