Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Bayelsa, Denis Otiotio, ya ce, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba dan jam’iyyar ba ne.
Otiotio ya bayyana hakan ga manema labarai a Yenagoa ranar Talata.
Sai dai ya ce jam’iyyar APC a shirye take ta tarbi tsohon shugaban kasar, idan har ya yanke shawarar komawa jam’iyyar.
“Tsohon shugaban kasa har yanzu bai zama dan jam’iyyar APC mai rijista ba. Yana da ‘yancin shiga duk jam’iyyar da ya ga dama.
“Muna a bayyane kuma a shirye muke mu karbe shi a cikin mu, a matsayinmu na jam’iyyar siyasa mai muradin cin zabe, hanya daya tilo ita ce shigar da mutane cikin jam’iyyar,” in ji shi.