fidelitybank

Jam’iyun adawa ne ke ingiza munate yin zanga-zanga – APC

Date:

Jam’iyya mai mulki ta APC ta zargi jam’iyyun adawar kasar nan da ingiza matasa su hau kan tituna da sunan zanga-zanga kan abin da ta bayyana da “nuna gwamnatin shugaba Tinubu da wadda ta gaza a tafiyar da mulki”.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar ta APC, Felix Morka ya fitar, jam’iyyar ta ce jerin zanga-zangar da aka yi a birnin Kano da Minna duka sun nuna irin zakuwar bangaren adawa na tunzura jama’a su yi wa gwamnati bore.

“Faruwar zanga-zangar a lokaci guda ba hakan nan ba. Alamu ne da ke nuni da kishirwar tayar da zaune tsaye domin yi wa gwamnati zagon kasa wanda kuma hakan ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.”, in ji sanarwar.

Mr Felix ya kara da cewa a daidai lokacin da gwamnati ta amince ‘yan kasa su nuna damuwarsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya to amma su yi hakan ta hanyar da ta dace da kuma doka ta tanada “sannan ka da su mika akalarsu ga ‘yan adawa da ke so yin amfani da su domin tayar da tarzoma”.

Daga karshe sanarwar ta bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnati shugaba Bola Tinubu na sane da halin da ‘yan kasa ke ciki kuma tana yin duk abin da za ta yi wajen tabbatar dda ta share musu hawaye.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp