Wata Hajiya daga jihar Kaduna ta rasu a asibitin ‘King Fahad’ da ke birnin Makkah.
Mai magana da yawun Hukumar Alhazan Jihar, Malam Yunusa Muhammad ne ya bayyana haka ga manema labarai a filin Arfa ranar Asabar.
Mallam Yunusa Muhammad ya ce tuni aka yi wa gawar hajiyar rajista hukumar Alhazan jihar.
Ya ƙara da cewa hukumar Alhazan jihar ta sanar da iyalan marigariyar labarin mutuwarta.
”Hukumar ta kuma jajanta wa iyalan marigariyar game da rashin nata”, in ji shi.
A yau ne dai aka gudanar da tsayuwar Arfa, ɓangare mafi muhimmanci a aikin Hajji.
Fiye da mutum miliyan 1.8 ne daui suka yi tsayuwar Arfar a yau Asabar.