A ranar Juma’a ne kotun koli za ta yanke hukunci kan shari’ar da ta samo asali daga rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC reshen Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa, jam’iyyar ta barke ne tsakanin bangarorin da ke biyayya ga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da kuma G-7 da tsohon gwamnan jihar Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta.
Wadanda suka shigar da kara a kotun koli su ne Musa Chola da wasu 1,319 kuma wadanda ake kara sun hada da APC, Gwamna Mai Mala Buni, Sanata John Akpanudoedehe, Olayide Adewale Akinremi, Sanata Abba Ali, Dr Tony Macfoy, Auwalu Abdullahi, Usman Kaita, Adebayo. Iyaniwura da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Wanda ya shigar da kara, wadanda ke biyayya ga G-7, sun samu nasara a kotun matakin farko (Babban Kotu), amma nasarar ba ta dade ba a lokacin da Kotun daukaka kara ta soke hukuncin da babbar kotun ta yanke, kuma ba tare da izini ba ta dawo da iko na jam’iyyar zuwa ga kungiyar Gwamna Ganduje.