fidelitybank

Jami’o’i: Ba mu karbi Naira biliyan 52 daga wajen gwamnati ba – ASUU

Date:

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta musanta karbar tsabar kudi Naira biliyan 52 daga wajen gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar ta ASUU shiyar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad ya bayyana hakan a ganawar sa da manema labarai, ya ce, kungiyar ta karbi Naira biliyan 22 daga gwamnatin tarayya, su ka yi amfani da kaso 75 cikin kudin, yayin da su ka raba kaso 25 ga sauran kungiyoyi da ke karkashin kungiyar.

Ya kara da cewa”Labarin da a ke yadawa cewa sun karbi Naira biliyan 52 karya ne, gwamnati ce ta fito da shi, domin batawa kungiyar mu suna, saboda kungiyar ta dage a kan sai an kawo gyara a harkar ilimi”.

Farfesa Abdulkadir Muhammad ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokari wajen kawo karshen matsalar tsaro dake addabar kasar nan.

Ministan kwadago, Chris Ngige ne dai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fitar da kudaden domin biyan malaman jami’an bashin alawus da albashi na fiye da watanni 20 da su ke bin gwamnatin.

dailysun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp