Wani jami’in zabe a Kenya wanda ke kula da mazaba guda a zaben da aka kammala a kasar ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi a ranar Litinin.
Geoffrey Gitobu, na cikin ofishin hukumar zabe da ke garin Nanyuki, a tsakiyar Kenya, a nan ne kawai aka ga ya yanke jiki ya fadi aka kwasheshi sai asibitin da ke kusa da ofishin kafin aje ma ya mutu.
Jami’in shi ne wanda aka tura daga hukumar zaben kasar don kula da zabukan mazabun Gichugu da kuma Kirinyaga da ke tsakiyar Kenya.
Rahotanni sun ce mr Gitobu, bai bayyana cewa bashi da lafiya ko kuma wani abu na damunsa ba, kuma sai da ya ziyarci wasu ‘yan uwansa a karshen mako kafin ya je ofishin zaben da ya yanke jiki ya fadi a can.
Wata jam’ar zabe da suke aiki tare Jane Gitonga, ta ce mutuwar abokin aikin na su ta girgiza su, kuma ya mutu ne kwanaki bayan kisan wani jami’insu a Nairobi.
Wata kwamishinar zabe a hukumar zaben kasar, ta ce jami’ansu na fuskantar barazana kala-kala tun bayan kammala zaben kasar a ranar 9 ga watan da muke ciki. In ji BBC.


