fidelitybank

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi daraktan tsare-tsare na fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, da karkatar da sama da naira biliyan 6.5 daga baitul-mali.

A wata sanarwa, da Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce, gwamnatin ta ce, duk kudaden dake fita daga asusun ta ana gudanar da su ne bisa kasafin kudi, ba tare da wani jami’i ya mallaki ikon kashe kuɗi yadda ya ga dama ba.

Sanarwar ta bayyana cewa zargin da aka wallafa a Daily Nigerian ya samo asali ne daga adawa da ke ƙoƙarin bata sunan gwamnati kafin 2027, tare da jaddada cewa Rogo mutum ne mai gaskiya da amana.

Gwamnatin ta kuma tunatar da yadda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kashe fiye da naira biliyan 20 cikin watanni uku kacal a shekarar 2023, tana mai cewa mutanen Kano sun san irin cin hanci da rashawa da taƙaita dukiya da aka yi a baya.

Wannan zargi ƙarya ce ta siyasa. Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta bar ƙoƙarin bata sunan jami’anta ya yi tasiri ba,” in ji sanarwar.

Gwamnati ta ce za ta ci gaba da gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana, tare da gargadin masu yada ƙarya da siyasar bata suna.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...
X whatsapp