Allah ya yi wa mataimakin shugaban kuma babban jami’in gudanarwar Max Air, Alhaji Bashir Barau Mangal rasuwa.
Bashir, kanin hamshakin dan kasuwa kuma shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a, a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, za a yi sallar jana’izar marigayin a Katsina da karfe 5:00 na yamma a yau.