Jami’ar Lincoln ta Burtaniya ta dakatar da wani dan majalisar dokokin Najeriya Ike Ekweremadu daga aikinsa na Farfesa mai ziyara.
Jamiāar Lincoln ta sanar da dakatar da Ekweremadu ne biyo bayan kama shi da laifin safarar mutane a kasar Birtaniya.
Cibiyar ta nada Ekweremadu a matsayin farfesa mai kula da harkokin kamfanoni da hadin gwiwar kasa da kasa da ya kai ziyara mako guda da ya gabata.
Jami’ar Lincoln ta ce, ba za ta kara yin tsokaci kan lamarin ba, har sai an kammala binciken ‘yan sandan Birtaniya kan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya da matarsa Beatrice.
A ranar Talata ne rundunar āyan sandan kasar Birtaniya ta kama Ekweremadu, dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Enugu ta Yamma, tare da matarsa Beatrice bisa laifin hada baki wajen girbe gabobin karamar yarinya.
An gurfanar da maāauratan tare da matarsa a gaban Kotun Majistare ta Uxbridge da ke Landan inda mai gabatar da kara ya bayyana cewa karamin yaro ne dan shekara 15 mai suna Ukpo Nwamini David.