Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, hukumomin tattara bayanan sirri na ƙasa sun ba shi kunya, bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata da dare.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da ya kai gidan yarin a ranar Laraba, kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
Shugaban ya shafe kusan minti 30 a gidan yarin, kuma ya yi tambayoyi da dama.
“Ta yaya jami’an tsaron da ke gidan yarin suka gaza daƙile harin? Fursunoni nawa ne a ciki? Guda nawa ne za a iya bayar da bayaninsu? Jami’ai nawa ne ke aiki lokacin da lamarin ya faru? Nawa ne ke ɗauke da makami?
“Masu gadin gidan yarin sun hau kan hasumiya? Shin kemarar tsaro tana aiki?” Duka waɗannan tambayoyin shugaban ya yi su a gidan yarin.
Bayan haka shugaban ya ce yana buƙatar a kai masa cikakken bayani kan yadda wannan lamarin ya faru.