Rundunar tsaron jihar Ogun, Amotekun, ta kama wani Ibrahim Ismaila bisa zargin yin lalata da wata akuya.
An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.
Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata.
Jimoh Opeyemi, ma’aikacin karfen karfe ne ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin yana barci da wata akuya.
Akinremi ya ce Opeyemi ya tayar da karar, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.
Kazalika, rundunar ta yi nuni da cewa ta kama wani Raimi Yusuf, bisa zarginsa da yin kwatankwacin wani jami’in Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta IBEDC.
An ce Yusuf ya damfari wasu mutane zunzurutun kudi har Naira miliyan 1.5.
An kama wanda ake zargin a Ijebu-Ode, ya ce, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi ma’aikaci ne na IBEDC, inda ya yi wa daya Olufeyisan Oluwaseun da wasu mutane hudu alkawarin gudanar da ayyukan samar da wutar lantarki da kuma mita daga kamfanin rarraba wutar lantarki.


