fidelitybank

Jami’an tsaro sun kashe ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Date:

Jami’an tsaro  sun kashe ‘yan fashin daji takwas tare da ƙwace babura yayin wani samame da suka kai a yankin Chikun da Birnin Gwari na Jihar Kaduna, a cewar gwamnatin jihar.

Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun rundunar rundunar haɗin gwiwa na Operation Forest Sanity ne suka ƙaddamar wa ‘yan bindigar cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.

“Dakarun sun gwabza da ‘yan fashin kuma suka kashe takwas daga cikinsu, sannan suka ƙwace babura huɗu da wayoyin hannu a samamen farko,” in ji shi.

Jami’an tsaron sun sake karawa da ‘yan bindigar a karo na biyu kuma suka ƙwace babur biyu.

A gefe guda kuma, dakarun sun yi nasarar kashe wasu ‘yan fashi biyu a yankin Sabon Birni da Maidaro da Dogon Dawa, duka a Jihar ta Kaduna.

A wannan karon ma, jami’an tsaro sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 da kuma harsasai da dama.

the sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe ƴan ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...
X whatsapp