Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wani Lawali Musa mai shekaru 36 dan kauyen Jangebe da kuma Jamilu Isah mai shekaru 40 dan yankin Yar dole na kananan hukumomin Talata Mafara da Gusau na jihar bisa zargin karbar kudi.
Kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya raba wa manema labarai a Gusau, ya ce an kama mutanen biyu ne biyo bayan korafin da mazauna kauyen ‘Yar Katsina da ke karamar hukumar Bungudu suka yi.
“A yayin da ake gudanar da bincike, babban wanda ake zargin, Lawali Musa ya amsa cewa ya karbo kudi naira miliyan biyar daga hannun al’umma da sunan taimaka musu wajen tura jami’an tsaro a yankinsu.
“A gefe guda kuma, wanda ake zargi na biyu, Jamilu Isah ya amsa cewa an saka kudi naira dubu dari takwas a asusun sa,” inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin cafke wasu da ake zargi da aikata laifin.
Ya ba da tabbacin za a gurfanar da su gaban kotu bayan gudanar da cikakken bincike domin fuskantar fushin doka.
“Rundunar ta yi amfani da wannan kafar wajen nanata cewa tura jami’an tsaro zuwa kauyuka da al’ummomi kyauta ne kawai,” in ji shi, yana mai kira ga kowa da kowa da kada ya bari wani mutum ko gungun mutane su yaudare su da sunan tabbatar da tura sojoji na jami’an tsaro zuwa yankunansu.
SP Shehu ya shawarci al’umma da su tuntubi ‘yan sanda ko duk wata hukuma da abin ya shafa game da tsaron yankunansu.


