Jami’an tsaro sun yi amfani da barkono mai sa hawaye a ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zanga waɗanda ke tattaki zuwa a kusa da fadar sarkin Kano da ke unguwar Nassarawa.
Tun da safe ne masu zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa suka fito a birnin, inda suka fara daga Gidan Murtala, suka ce za su yi tattaki zuwa gidan gwamnati.
Da farko zanga-zangar ta fara cikin lumana, sai dai daga baya abubuwa sun fara rincaɓewa a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin tarwatsa masu zanga-zangar wadanda suka dumfari gidan gwamnati.
Bayanai na cewa jami’an tsaro sun yi harbi da bindiga a kan masu zanga-zangar.


