Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, reshen jami’ar Ibadan, ta bukaci jami’an tsaro da su daina bata lokaci wajen zakulo wadanda suka kashe daya daga cikin mambobinta.
ASUU ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, bayan hallaka, Farfesa Opeyemi Isaac Ajewole na sashen raya gandun dazuzzuka na jami’ar Ibadan da aka yi wanda har yanzu ba a tantance ko waye ba.
ASUU ta shaidawa Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba da ya taimaka wa rundunar ‘yan sandan jihar Oyo da duk wani tallafin kayan aiki da ake bukata domin bankadowa tare da kamo wadanda suka kashe don.
Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta Farfesa Ayo Akinwole.
Akinwole, a cikin sanarwar da aka rabawa manema labarai, ya baiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu aiki da ya jajirce wajen ganin jami’an tsaro sun bankado fuskokin da suka yi kisan mamacin.
Ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Adewole gaba daya.