fidelitybank

Jami’an tsaro na farautar mai magana da yawun Gwamnan Kano

Date:

Akalla jami’an tsaro 40 ne daga Abuja ke ci gaba da neman mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature Dawakin-Tofa kan labarin dakatar da Ganduje.

An tura mutanen IGP din ne daga Abuja domin kama Dawakin-Tofa bisa umarnin mukaddashin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Dr Abdullahi Ganduje.

Ganduje dai ya kai karar IGP ne kan cece-kucen da ya biyo bayan dakatar da shi da aka yi daga shiyyarsa ta Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin-Tofa a jihar, inda ya zargi Kakakin Gwamnan da ya fito daga mazabarsa da kitsa rikicin siyasa.

Majiyoyin iyalan sun shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, tawagar ‘yan sandan da ke sanye da fararen kaya, sun sanya ido a kan gidan Dawakin-Tofa a ranar Litinin a wani mataki na gudanar da aikin nasu.

Daya daga cikin ‘ya’yan gidan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan sandan sirrin sun yi wa gidan farmaki sama da sau 5, lamarin da ya tsoratar da ‘yan gidan Dawakin-Tofa da suka hada da mata da ‘ya’ya tare da haifar da fargaba a unguwar.

Rundunar ‘yan sanda ta musamman ta IGP ta daura damarar kama Sanusi Dawakin-Tofa a cikin makonni biyun da suka gabata duk da umarnin da kotu ta bayar na hana su IGP, DSS, CP Kano da sauran hukumomin tsaro daga kamawa ko kuma musgunawa mai magana da yawun gwamnan.

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu na babbar kotun jihar Kano a ranar Alhamis ta amince da bukatar da ta ke yi na hana ci gaba da farautar Sanusi Dawakin-Tofa har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren wasu muhimman batutuwa game da hakkokinsa da aka tsara ranar 22 ga watan Janairun 2025.

Rikicin da ke tsakanin Dawakin-Tofa da Ganduje, ya samo asali ne tun shekaru tara da suka gabata, musamman a shekarar 2015, lokacin da Ganduje a matsayin zababben gwamna, ya bayar da umarnin a kamo Dawakin-Tofa saboda adawar da ya yi a lokacin zaben gwamna.

A kwanakin baya ne dai Ganduje ya kai karar IGP, inda ya zargi Dawakin-Tofa da cewa shi ne ke da alhakin dakatar da shi da shugabannin jam’iyyar APC Ganduje suka yi a watannin baya.

Sakamakon haka, an tattaro tawagar jami’an ‘yan sanda 40 daga sashin sa ido na IGP zuwa Kano da nufin cafke mai magana da yawun gwamnan.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan hedikwatar ta kasa FPPRO ya ci turaJami’an

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp