fidelitybank

Jami’an tsaro ku kara kaimi a bangaren tsaro – Sarkin Kano

Date:

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen dakile munanan laifuka a jihar.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon kwamishinan ‘yan sandan da aka nada a fadar sa a ranar Asabar.

Alhaji Ado Bayero, wanda Walin Kano, Alhaji Bashir Mahe ya wakilta, ya bukaci jami’an ‘yan sanda da su yi aiki da tsoron Allah da kuma aiki tukuru kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada da kuma dokar ‘yan sanda ta shekarar 2020.

Ya bukaci hukumomin tsaro da su mutunta ‘yancin dan adam, bin doka da oda da kuma yin aiki bisa kyawawan halaye na kasa da kasa.

“Muna ba ku tabbacin goyon baya, addu’o’i, da taimakon dukkanin cibiyoyin gargajiya a fadin jihar,” in ji shi.

Tun da farko kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mamman Dauda ya bayyana cewa manufarsa ta zuwa fadar sarkin ita ce don gabatar da kansa ga sarkin da kuma neman addu’a, hadin kai, da shawarwarin uba don ‘yan sandan jihar Kano yadda ya kamata.

“Za mu ci gaba da yin aiki gwargwadon iyawarmu don tabbatar da zaman lafiya a jihar,” in ji CP.

latest nigeria newstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...
X whatsapp