Majalisar Dattijai ta buƙaci rundunar sojojin ƙasar nan da sauran hukumomin tsaro su ƙaddamar matakan katse hanzarin ƙungiyar ƴan bindigar nan ta Lakurawa.
Majalisar ta kuma yi kira da a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin hana su faɗaɗa ayyukansu a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Ta kuma nemi a ci gaba da sa-ido a yankunan da Lakurawan suka mamaye, inda ta yi gargaɗin cewa a ɗauki matakan da suka dace, domin a cewarsu, haka Boko Haram ta fara.
Lakurawa dai ƙungiyar ƴanbindiga ne da suka daɗe suna zuwa wasu yankuna na jihohin Sokoto da Kebbi, inda yanzu harkokinsu suka fara ta’azzara.