fidelitybank

Jami’an tsaro ku gaggauta kamo makasan Sarkin Gobir – Ministan Tsaro

Date:

Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya sha alwashin cewa za a zaƙulo tare da hukunta duk masu hannu a kisan Sarkin Gobir na Gatawa da ke jihar Sokoto, Isa Bawa.

A ranar Laraba ne labarin kisan sarkin ya fito bayan ya kwashe sama da mako uku a hannun ƴan bindiga.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktar ƴaɗa labaru ta ofishin ministan, Henshaw Ogubike, Matawalle ya yi tir da kisan sarkin, tare da bayyana hakan a matsayin “aikin rashin imani kuma abin da ba za a amince da shi ba.”

Ya ƙara da cewa “za mu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu domin ganin an hukunta waɗanda ke da laifi a lamarin”.

Takardar ta ce Matawalle ya umarci shugaban hafsoshin tsaron Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan kisan nan take tare da tabbatar da ganin an hukunta duk wadanda ke da hannu cikin lamarin.

Ta ƙara da cewa “za mu yi bincike na ƙwaƙwaf wajen ganin an hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.”

A jiya Alhamis ne dai aka gudanar da sallar janaza ta ‘Salatul Ga’ib’, ga sarkin na Gobir, wanda ƴan bindiga suka hallaka, kasancewar ba a samu gawarsa ba.

Sai dai an samu nasarar karɓo ɗan marigayin, wanda ƴan bindiga suka ce su tare, wanda yanzu haka yake karɓar kulawa a asibiti.

Matsalar masu satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da addabar jihohin arewa maso yammacin Najeriya, duk kuwa da ƙoƙarin da hukumomi suka ce suna yi wajen tabbatar da tsaro.

Sai dai kisan sarkin na Gobir na daga cikin munanan abubuwan da suka faru a kwana-kwanan nan da ke nuna cewa har yanzu ƴan bindigar na ci gaba da cin karensu babu babbaka.

nigerian 
newspapers today the sun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp