fidelitybank

Jami’an So Safe Corps ta kama masu hakar ma’adanai a Ogun

Date:

Jami’an hukumar tsaro na So-Safe Corps mallakin jihar Ogun, sun kama wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba har su 12 a yankin Ogun ta Gabas.

An kama mutanen 12 a tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga watan Satumba, “a lokacin da suke satar dukiyar gwamnatin jihar.”

Kakakin Rundunar So-Safe, Moruf Yusuf, ya shaida wa wakilinmu cewa, an tsare masu hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba ne a kauyen Abeku Adekanmbi da ke karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar Ogun.

Yusuf ya bayyana cewa an kama mutanen 12 “a lokacin da suke satar albarkatun ma’adinai kamar gawayi da zinare a karkashin kasa.”

A cewarsa, Kwamandan So-Safe, Soji Ganzallo, ba tare da bata lokaci ba, ya ba da umarnin a mika rahoton binciken farko na wadanda ake zargin zuwa hedikwatar hukumar ta jihar da ke Abeokuta.

Ganzallo ya kuma bayar da umarnin a gurfanar da sauran masu laifin da suka tsere ta hanyar babura.

Tuni dai aka mika wadanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Ijebu Igbo domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya, in ji Yusuf.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp