fidelitybank

Jami’an mu ba su yi murabus ba – Sojoji

Date:

Rundunar Sojin ƙasar nan, ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami’anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala.

A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci “da ya yi wa aikin katutu”.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan.

A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta.

Sanarwar ta kara da cewa: “Batun cewa sojoji na yin murabus daga muƙamansu saboda rashin jin dadin rayuwa, da cin hanci da rashawa ba gaskiya ba ne.”

Rundunar ta fayyace cewa jami’anta suna da ‘yancin yin murabus daga muƙamansu bisa raɗin kansu, bisa ga ka’idojin da aka tsara a cikin ƙa’idojin Hidima na Hafsa da Sojoji.

Rundunar Sojin ta kuma bayyana ci gaba da jajircewarta na jin dadin ma’aikatanta a ƙarkashin jagorancin babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Daga ƙarshe rundunar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tantance bayanai kafin a buga su don hana yaɗa labaran da ba su da tushe da makama

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp