Jamiāan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, sun kama mutane 34 da ake zargi da hannu a samamen da suka kai a wuraren da aka haramta safarar miyagun kwayoyi a babban birnin tarayya Abuja.
Kwamandan hukumar na babban birnin tarayya Abuja, Kabir Tsakuwa, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa an gurfanar da wasu daga cikin wadanda ake zargin, yayin da wadanda aka bayyana cewa masu amfani da su ne ake yi musu nasiha.
Ya bayyana cewa ya zama wajibi a gudanar da aikin ne domin yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi, musamman a lokacin da Najeriya ke shirin mikawa sabuwar gwamnati.
Ya kuma bayyana cewa, rundunar ta kaddamar da āOperation Tsaroā ne a ranar 8 ga watan Mayu domin rufe cibiyoyin shan magani tare da damke dillalai a babban birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, “Jami’an mu sun kama wasu haramtattun abubuwa da suka hada da cannabis sativa, methamphetamine, tramadol, codeine, Rohypnol, da sauran abubuwan da suka shafi kwakwalwa.”
Tsakuwa ya ba da tabbacin ci gaba da kai farmakin da nufin dakile ayyukan taāaddanci a babban birnin tarayya Abuja a matsayin hanyar rage yaÉuwar miyagun kwayoyi.
Ya bayyana cewa wasu wuraren da aka kai farmakin sun hada da Torabora, Dei-dei, Wuse Zone 4, Wuse Zone 3, Banex, Garki Village Area 1, Gwarinpa (Village, 3rd Avenue), Abattoir a Karu, Gwagwalada, Kabusa, da Kuchigoro. IDP Camp.