Ministocin gwamnati a Birtaniya sun shafe daren Laraba suna ganawa da Firaminista Boris Johnson a fadarsa, gida mai lamba 10 Titin Downing, domin su lallaba shi ya sauka daga mukaminsa.
Hakan na zuwa ne a yayin da sauran goyon bayan da yake da shi a jam’iyyar Conservative mai mulkin kasar ke raguwa.
BBC ta gano cewa, daya daga cikin makusantansa, Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel – na cikin wadanda ke lallaba shi ya yi murabus.