Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi Allah wadai da satar ɗalibai a jihar Kaduna da ƴan gudun hijra a Borno tare da bayar da umarnin a gaggauta ceto su.
Mai taimaka wa shugaban ƙasar na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a wata sanarwa ya ce shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta ceto ɗaliban da ƴan gudun hijirar da kuma hukunta masu hannu a lamarin.
Sanarwar ta ayyano shugaban Najeriyan ya na cewa “Shugabannin hukumomin tsaro sun yi mani bayani a kan abin da ya faru a Borno da Kaduna kuma ina da yaƙinin cewa za a ceto su.”
Shugaba Tinubu ya ce ba zai lamunci duk wani uzuri ba har sai an ceto yaran da aka yi garkuwa da su.
Ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin dawo da ƴaƴansu.