Mahukunta a Jamhuriyar Benin sun ce ƙasar za ta karɓi kashin farko na rigakafin zazzaɓin cizon sauro – cutar da ke kan gaba wajen haifar da mutuwar yara ƙanana a ƙasar, kuma nan ba da jimawa ba za a fara yin rigakafin.
Ministan lafiya na Benin, Benjamin Hounkpatin ya shaida wa manema labarai a filin jirgin sama na Cotonou cewa, maleriya cuta ce da ke yawan addabar mutane a ƙasar.
Ya ce gwamnati a hukumance, ta karɓi allurai 215,900 na rigakafin cutar.
A cewarsa za a soma ba da allurar nan da wasu ƴan watanni.
A ƙasar ta Benin, kashi 40 cikin 100 na masu zuwa asibiti da kashi 25 cikin 100 na mutanen da aka kwantar na da alaƙa da zazzabin cizon sauro, a cewar ministan.
Ya ce jarirai za su karɓi alluran sau huɗu – suna wata shida da wata bakwai da wata tara da kuma wata 18.
Benin ce ƙasar Afirka ta uku da ta samu alluran rigakafin maleriya bayan Kamaru da Saliyo, bayan da aka ƙaddamar da shirin a Ghana da Kenya da Malawi ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya ta duniya bisa tallafin shirin kawance kan alluran rigakafi na GAVI.
An yi wa yara fiye da miliyan biyu rigakafin cutar a waɗannan ƙasashen Afirka uku abun da ya kawo raguwar mace-macen da ke da nasaba da maleriya, kamar yadda shirin GAVI ya bayyana.
A cewar WHO, kusan kowane minti guda, ana samun yara ƴan ƙasa da shekara biyar da ke mutuwa sanadin cutar.


