Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James Trafford ya sake komawa kungiyarsa ta Manchester City.
Ya kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar kaka biyar da kungiyar Etihad, wadda ya bari a 2023 ya koma Burnley.
Trafford wanda zai sa riga mai lamba daya – ya zama na shida da City ta dauka a kakar nan bayan Rayan Ait-Nouri, Tijjani Reijnders da Marcus Bettinelli da Rayan Sherki da kuma Sverre Nypan.
Trafford ya fara City daga 2015 daga nan aka bayar da aronsa ga Accrington da Bolton daga baya ya kasa samun buga wasanni a kungiyar Etihad saboda Ederson hakan ya sa aka sayar da shi kungiyar Turf Moor.