Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, ta kara kudin rajistar jarrabawar shiga jami’a, UTME.
Hukumar jarrabawar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.
Ta amince da kudi naira dubu bakwai da dari bakwai, (N7,700) a matsayin kudin jarabawar UTME. Har ila yau, ta sanya kudin jarabawar gwaji, Naira dubu shida da dari biyu, N6200.
Hukumar ta kuma ce a yanzu za a samu takardun neman zana jarabawar daga kasashen waje a kan dala 30.