Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta bayyana a ranar Alhamis cewa jami’o’i da sauran manyan makarantun kasar nan na iya karbar ɗalibai da za su cika shekaru 16 kafin ranar 31 ga watan Agustan 2025.
Hukumar ta sanar da cewa za a iya shigar da ‘yan takarar da abin ya shafa don zaman karatun 2024/2025 idan sun cika ka’idojin makarantar.
Ku tuna cewa mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu an fara tattaunawa a farkon wannan shekara a taron Siyasa na 2024 kuma an yanke shawarar zama shekaru 16 don zaman karatun 2024/25.
Wannan ci gaban ya jawo martani daga iyaye da sauran ‘yan kasar da abin ya shafa, wadanda suka bayyana ra’ayoyi mabambanta kan lamarin.
Sai dai a wata sanarwa da hukumar ta JAMB ta fitar a ranar Alhamis ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Fabian Benjamin, ta ce saboda wasu cibiyoyi sun tsawaita wa’adin shiga jami’o’in zuwa watan Yulin shekarar 2025, za ta baiwa cibiyoyi damar karbar wadanda za su cika shekaru 16 kafin ranar 31 ga watan Agustan 2025.
“Wannan kokarin shine don tabbatar da daidaito saboda wadanda aka shigar da su a shekarar 2024 har zuwa watan Agusta 2025 ba za su sami tagomashi ba. Sanarwar ta kara da cewa, duk wata cibiya da ta dage a kan shekaru 16 da ta yi a cikin shekarar 2024, tana da ‘yancin yin hakan.