Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami’o’i ta Najeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar.
Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar da babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Haka kuma hukumar ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin sabun gurbi kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100.
An dai samu gagarumar faɗuwa a jarawabar JAMB da aka rubuta a wannan shekara.