fidelitybank

Jakadiyar ECOWAS za ta gana da Tinubu kan makomar Nijar

Date:

Mataimakiyar sakataren harkokin ƙasashen Afirka ta Amurka, Molly Phee ta ziyarci Najeriya domin shiga tsakani kan rikicin shugabancin Nijar, wadda ke ƙarƙashin mulkin soji tun ranar 26 ga watan Yuli.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta nuna cewa Ms Phee za ta tattauna da shugaban Najeriya Bola Tinubu, tare da shugabannin ƙungiyar Ecowas kan rikicin siyasar Nijar.

Sanarwar ta ce an tsara ganawa tsakanin jakadiyar Amurkan da shugabanin ƙasashen ƙungiyar Ecowas ranar Litinin 10 ga watan Disamba domin tattauna batun.

“A lokacin ziyarar tata, za ta tattauna da shugabannin Afirka da Yamma, kan yadda Amurka za ta tallafa wajen maido da mulkin dimokraɗiyya a jamhuriyar Nijar, tare da inganta tsaro da zaman lafiya da ci gaban yankin, da kuma tabbatar da dimokraɗiyya a yankin sahel,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Ziyarar Ms Phee Najeriya na zuwa ne watanni huɗu bayan da sojojin Nijar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani suka kifar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.

Juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli ya sha suka da Allah wadai daga ƙasashen duniya, yayin da ƙasashen Yamma suka nuna goyon bayansu ga ƙungiyar Ecowas da ta AU, waɗanda suka nuna adwarsu ga juyin mulkin.

Inda ƙungiyar Ecowas ƙarƙashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Tinubu ta ƙaƙaba wa Nijar jerin takunkuman karya tattalin arziki, don tilasta wa sojojin mayar da shugaba Bazoum kan karagar mulki.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp