Shugaban haramtacciyar kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya isa babbar kotun tarayya da ke Abuja domin sake gurfanar da shi.
Kanu wanda ke sanye da farar riga, jamiāan tsaro ne suka shigar da shi cikin kotun da misalin karfe 10 na safe.
Ana tuhumar shugaban ‘yan awaren bisa zargin ta’addanci.
A cewar lauyoyinsa, ya shirya tsaf domin halartar zaman kotun saboda yana cikin koshin lafiya.
A halin da ake ciki kuma, birnin Aba da ke jihar Abia ya kasance cikin kulle-kulle don nuna goyon baya ga Kanu, wanda za a gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau (Talata).
Titin Aba gaba daya babu kowa yayin da mazauna gida ke ci gaba da zama a gida bisa bin umarnin zaman-gida.
Babu motsin ababen hawa sai ʓan motoci da ke wucewa lokaci-lokaci.
Babu kasuwa ko shago da aka buÉe a kusa da birnin yayin da mazauna gida ke zama a gida.
Bankunan da makarantu, na masu zaman kansu da na gwamnati, duk an rufe su.