fidelitybank

Jagoran Venezuela ya yi balaguro zuwa Spain

Date:

Gwamnatin Venezuela ta ce ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar adawa, Edmundo González, ya fice daga ƙasar zuwa Sifaniya domin neman mafaka.

Cikin wani saƙo da mataimakiyar shugaban ƙasar, Delcy Rodríguez, ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta ce ”bayan neman zaman gudun hijira da ya yi bisa raɗin kansa a ofishin jakadancin Sifaniya da ke birnin Caracas a kwanakin da suka gabata, mista Gonzalez ya nemi gwamnatin Sifaniya ta ba shi mafakar siyasa”.

Ta ƙara da cewa gwamnatin Venezuela ta amince da ficewarsa daga ƙasar, kuma tuni ya yi hakan.

Ministan harkokin wajen Sifaniya, José Manuel Albares, ya ce Mista González ya fice daga Venezuela ne bisa raɗin kansa, kuma ya fice ne a jirgin rundunar sojin Sifaniya.

Mista González ya kasance yana wasan ɓuya da jami’an tsaro a Venezuela, bayan da aka bayar da sammacin kama shi sakamakon zaɓen shugabar ƙasar da ya gabata mai cike da taƙaddama.

Hukumar zaɓen ƙasar dai ta ayyana shugaba Nicolás Maduro a matsayin wanda ya lashe zaɓen, duk da ayyana samun nasara da mista González ya yi, gabanin sanarwar hukumar zaɓen ƙasar.

fg spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp