Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana gaban jama’a a karon farko tun soma yaƙi tsakanin ƙasarsa da Isra’ila, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka shaida.
Wani hoton bidiyo daga gidan talabijin na Iran ya nuna jagoran yana gaisawa da masallata a wani masallaci ranar Asabar yayin wani biki gabanin bikin Ashura na Mabiya shi’a.
Fitowa ta ƙarshe da Khamenei ya yi ita ce bayyanarsa a wani jawabi da aka naɗa a lokacin da ake tsaka da yaƙi da Isra’ila da aka soma ranar 13 ga watan Yuni wanda kuma a lokacin aka kashe manyan kwamandojin Iran da masana kimiyyar nukiliya.
Isra’ila ta ƙaddamar da wani harin ba-zata kan cibiyoyin nukiliyar Iran lamarin da yasa Iran ɗin ta mayar da martani da hare-hare ta sama kan Isra’ila.