Jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah yana gabatar da jawabi tsawon ‘yan mintuna kalilan yanzu.
Yana yabawa hare-haren da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba a kan Isra’ila, wanda ya yi sanadin kashe fiye da mutum 1,400.
Wakilin BBC a yankin Gabas ta Tsakiya na kallon jawabin kuma za mu kawo muku sharhi kan abin da ya ce da kuma abin da hakan ke nufi kan yakin da ake ci gaba da gwabzawa.
A yanzu kuma, ga bayani game da jagoran wanda ba a cika gani a bainar jama’a ba, na kungiyar da Birtaniya da Amurka da Isra’ila da kuma karin wasu kasashe, suka ayyana a matsayin ta ‘yan ta’adda.
Malamin mai bin mazhabar Shi’a, shi ne ke jagorantar Hezbollah tun daga 1992, kuma Nasrallah ya ba da gagarumar gudunmawa wajen mayar da ita kungiyar siyasa da runduna mai karfin soja.
Yana da alaka ta kukut da kasar Iran da kuma jagoran addininta, Ayatollah Ali Khamenei, tun daga 1981, lokacin da jagoran addinin Iran na farko, Ayatollah Ruhollah Khomeini, ya nada shi wakilinsa na musamman a Lebanon.
Tsawon shekaru kenan, ba a ga Nasrallah a bainar jama’a ba, kamar yadda ake zargi saboda tsoron kada Isra’ila ta hallaka shi.
Sai dai ya kasance abin matukar martabawa daga Hezbolla kuma yana gabatar da jawabansa ta talbijin a duk mako.