Hukomomin Saudiyya sun dawo da Alhazan Kano bakwai gida daga kasar, saboda sun yi amfani da bizar bogi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, biyar daga cikinsu sun je Saudiyya ne ta hanyar kamfanonin shirya tafiye-tafiyen aikin hajji masu zaman kansu, sai kuma biyu wadanda suka je ta hannun hukumar alhazan jihar Kano.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, ba su san bizar bogi aka ba su ba, sai bayan da suka isa Saudiyya.
”Muna kan layin tantancewa da aka zo kaina sai aka ce na koma gefe, daga nan kuma suka shaida mana cewa bizar bogi muke dauke da ita”, in ji shi.