Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana atisaye shi kaɗai a tsohuwar ƙungiyarsa ta Real Socieded, yayin da ake cigaba da cece-kuce game da makomarsa a ƙungiyar kafin fara kakar wasa ta bana.
Ɗanwasn na ƙasar Sweden mai shekara 25 bai samu shiga tawagar Newcastle da ta je nahiyar Asiya ba saboda ƙaramin rauni a cinyarsa kamar yadda kulob din ya bayyana.
Isak na son ya bar Newcastle kuma ana kyautata zaton Liverpool ce kan gaba wajen neman ɗauke shi daga filin wasa na St James’ Park.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa, ɗanwasan na yin atisaye ne shi kaɗai a Socieded ba tare da sauran tsofaffin abokan wasansa ba.
Ya koma Newcastle daga Socieded kan fan miliyan 60 a 2022.